
BBC News Hausa
@bbchausa • 2,555,050 subscribers
BBC Hausa - Fiye da shekara 60 na labaran duniya da rahotannin da suka shafi rayuwarku
Shorts
Videos

Usman Muhammad da matarsa Fatima sun haɗa kai wajen noma a gonar ayabar mijin domin samun kuɗi, har ma suna amfani da asusun banki guda ɗaya wajen tafiyar da harkokinsu na kuɗi. Ga yadda suke gudanar da aikin gonar cikin lumana da haɗin kai. 🎥 - Abba Auwalu
BBC News Hausa194,209 Aufrufe • vor 15 Tagen

Me ya sa Hajiya Amina Mohammed ba ta ɓoye asalinta na Bahaushiya a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma wane tasiri tasowarta a Arewacin Najeriya ya yi ga rayuwarta? Hajiya Amina ta yi ƙarin bayani a hirarta da BBC. 📷 - Benz Wasawat Lukharang Tace Hoto - Fatima Othman
BBC News Hausa52,879 Aufrufe • vor 8 Tagen

Mahaifiyar tagwayen da suka rasu cikin sa’o’i 48 a Yobe ta ce bayan rasuwar Hadiyah, ’yar uwarta A’ida ta riƙa cewa ba za ta iya rayuwa ba tare da ’yar uwarta ba, kafin ita ma ta rasu. A tattaunawarta da BBC, mahaifiyar ta bayyana yadda ta ji da rashin. Take hoto - Abba Auwalu
BBC News Hausa76,560 Aufrufe • vor 16 Tagen

Yayin da ya rage ƙasa da watanni uku kafin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, batun tallafin mai na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da za su iya tasiri kan yadda zaɓen zai gudana. 📸 - Isiyaku Muhammed/Nabeela Mukhtar Uba #BBCHAUSA #nigeria #petrol
BBC News Hausa11,079 Aufrufe • vor 2 Tagen

Mahaifin da ya rasa ’ya’yansa uku bayan da ruwa ya tafi da su a wani kogi a Abuja ya bayyana wa BBC irin raɗaɗin rashin ’ya’yansa. Aliyu Abubakar, mahaifin yaran, ya ce an gano gawarwakin biyu daga cikin yaran, amma har yanzu ba a gano na ukun ba. 🎥 — Abba Auwalu
BBC News Hausa64,407 Aufrufe • vor 14 Tagen

Kun san yadda tarukan Babban Bankin Duniya da IMF za su iya shafar rayuwarku? Madina Maishanu ta halarci taron don gano yadda shawarwarin da za a yanke za su iya shafar tattalin arzikin ƙasarku da kuma farashin kayan abinci. 📸: Benz Wasawat Lukharang Tace hoto: Fatima Othman
BBC News Hausa51,826 Aufrufe • vor 13 Tagen

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya shaida wa BBC dalilan da suka sa ya jaddada niyyarsa ta mayar da tallafin man fetur a Najeriya idan ya ci zaɓen 2027. Ya kuma bayyana manyan abubuwan da yake sa ran yi domin inganta rayuwar ʼyan Najeriya da kawar da matsalar tsaro.
BBC News Hausa148,562 Aufrufe • vor 1 Monat

Atiku Abubakar ya shaida wa BBC dalilan da suka sa ya jaddada niyyarsa ta mayar da tallafin man fetur a Najeriya idan ya ci zaɓen shugaban ƙasar Najeriya a 2027. Ya kuma bayyana manyan abubuwan da yake sa ran yi domin inganta rayuwar ʼyan Najeriya da kawar da matsalar tsaro. 📷 - Abba Auwalu Furodusa - Aminu Kutama
BBC News Hausa117,188 Aufrufe • vor 1 Monat

Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya faɗi manyan abubuwan da suka sa aka kasa shawo kan matsalar tsaro a ƙasar da kuma salon da zai yi amfani da domin kawo ƙarshen matsalar. Ya kuma bayyana aniyarsa ta gina katanga a wasu iyakokin Najeriya.
BBC News Hausa372,361 Aufrufe • vor 9 Monaten

Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke bayan mutuwar kimanin mutum 37 a ofishin hukumar tsaro ta NSCDC. Mun yi bayani game da dalilin da ya janyo mutuwar matasan. 📸 - Aisha Aliyu Jaʼafar
BBC News Hausa56,245 Aufrufe • vor 1 Monat


